| Name | : | islamkingdom_ar |
| Website | : | Visit Website |
| Blog | : | Visit Blog |
| Social Links | : |
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Haxa ayyukan duniya da ayyuka na qwarai : Manzon Allah (S.A.W) ya ce, �A cikin tarawar xayanku da iyalinsa akwai ladan sadaka. Sai suka ce, ya Manzon Allah, yanzu xayanmu zai biya sha�awarsa kuma ya zama yana da lada? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, �Ku ba ni labari idan ya sanyata a haramun yana da alhaki? To haka ma idan ya sanyata a halal, to yana da lada� (Muslim ne ya rawaito shi) Korar munanan saqe-saqen Shaixan da wasiwasinsa : Yayin da Allah ya kori Shaixan ya nisantar da shi daga rahamarsa sai Allah ya faxa mana abin da ya ce, �Ya ce, ya Ubangijina saboda vatar da ni da ka yi, sai na qawata musu (Varna) a bayan qasa gabaxayansu. Sai dai bayinka cikinsu waxanda aka tsarkake� (Alhijri : 39 � 40) Ta yi wu wani ya nisanci duniya da jikinsa, amma kuma yana tare da ita a zuciyarsa. Ta yiwu wani kuma yana tare da duniya da jikinsa, amma kuma baya tare da ita da zuciyarsa, wannan shi ya fi hankali.
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Na huxu : Ka watsar da son yabon mutane daga zuciyarka, ka xebe qauna daga abin da yake hannun mutane, ka mayar da komai naka zuwa ga Allah mai girma da buwaya. Mai tsarkake niyya mai yin abu don Allah baya kwaxayin wata duniya da zai samu, ko wata mace da zai aura, kwaxayinsa kullum shi ne rahamar Allah. Na biyar : Ka koma ka faxi gaban Ubangijinka, ka lazimci bakin qofarsa mai girma da buwaya tare da yin addu�a Allah ya azurtaka da tsarkin zuciya, da barin riya, ya karvi tubanka daga abin da ya gabata na zunubai da savo. Tsarkake niyya shi ne kada nemi wani ya san aikinka sai Allah, kada ka nemi wani sakamako daga wajen waninsa Na shida : Nisantar riya da guje mata, Idan bawa ya shigar da kansa hanyar riya to ya qara nisa daga hanyar Allah. Misalin haka yadda wasu mutane suke kiran kawunansu da waliyyi, ko mutum ya yarda a kira shi da haka, ko ya riqa bayar da labarun ayyukansa da biyayyarsa ga Allah. Allah yana cewa, �Waxanda suke neman rayuwar duniya da adonta to za mu cika musu
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Matsayin Ikhlasi Ikhlasi yana da matsayi babba a addini, wanda babu abin da ya kai shi matsayi, ba a karvar aiki sai da tsarkake niyya, Allah Maxaukakin Sarki ya tunatar da mu Ikhlasi a wurare da dama a cikin Alqurni mai girma, daga ciki akwai faxin Allah Maxaukakin Sarki �Ba a umarce su sai dai su bautawa Allah suna masu tsarkake addini gare shi� (Albayyinah : 5) Kuma Allah mai girma da buwaya ya ce, �Ka ce haqiqa sallata da yankana da rayuwata da mutuwata na Allah ne Ubangijin talikai. Ba shi da abokin tarayya, da wannan aka umarce ni, nine farkon musulmi� (Al�an�am : 162 � 163) Allah mai girma da buwaya ya ce, �Wanda ya halicci mutuwa da rayuwa don ya jarrabeku wanene a cikinku ya fi kyan aiki� (Al-mulk : 2) Kuma Ya sake cewa : �Haqiqa mun saukar maka da littafi da gaskiya, ka bautawa Allah kana mai tsarkake masa addini, ku saurara addini. Tsarkakakken addini na Allah ne� (Azzumar : 2 � 3) Kuma Ya ce, �Wanda yake fatan gamuwa da Ubangjinsa to ya yi aiki na qwarai kada ya haxa wa
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Allah Mai Bayarwa Mai Hanawa Lallai Shi ne Allah mai bayarwa mai hanawa Godiya ta tabbata ga Allah wanda yake kamar yadda ya siffata kansa, sama da yadda halittarsa suka siffata shi. Imam Shafi�i �Allah mai bayarwa mai hanawa�.. Ba wanda zai hana abin da ya bayar, ba kuma mai ba da abin da ya hana, dukkan wata maslaha da amfani a wurinsa ake nema, a wurinsa ake kwaxayinsu, shi ne mai bayarwa ga wanda ya ga dama, yana hana wanda ya ga dama da hikimarsa da rahamarsa. Ya mai shimfixawa, shimfixa mana daga rahamarka, ka ba mu daga kyautarka, ka kame mana mummuna ya mai kamewa, ka kare mana sharri da mummuna ya wanda yake hanawa.
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Allah Mai Riqewa Da Shimfixawa Shi ne Allah mai riqewa da shimfixawa �Allah Mai Riqewa� Ya riqewa wasu mutane arzikinsu don ya jarrabe su. Yana hana wasu don ya tanqwara su, ya tsare na wasu nasu don ya xaukaka su. �Allah Mai Shimfixawa� Ya shimfixa arziki, ya shimfixawa zukata saninsa, duk wannan da hikimarsa da rahamarsa da kyautarsa, tsarki ya tabbata a gare shi. Lallai Shi ne Allah mai riqewa da shimfixawa
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Allah maxaukaki mafi xaukaka Shi ne Allah maxaukaki mafi xaukaka. Maxaukaki Mai xaukaka.. Yana da xaukaka a akan dukkan bayinsa, xaukakar zati, da xaukakar daraja, da xaukakar siffa, da xaukakar rinjaye.. (Shi ne Maxaukaki mai girma) (Albaqra : 255) Ya daidaita a kan al�arshi, da dukkan siffofin girma da xaukaka da kyau, da cikar kamala ta qarshe da nuna isa.
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Allah sha yabo, mai girma, mai xaukaka Shi ne Allah abin yabo da girma da xaukaka Shi ne Allah wanda ya siffatu da siffofin girma, da xaukaka, wanda ya fi komai girma, ya fi komai xaukaka. Yana da girma da xaukaka a cikin zukatan masoyansa zavavvun bayinsa. Zukatansu sun cika da girmansa da xaukakarsa, da qasqantar da kai gare shi. Tsarki ya tabbata gareka. Ya girma mene ne ya yi girmanka!!... �Ka tsarkake sunan Ubangijinka mai girma� (Alwaqi�a : 96)
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Allah Sha Yabo Haqiqa shi ne Allah sha yabo Abin yabo a zatinsa, abin yabo a ayyukansa, abin yabo a halayensa, abin yabo a maganganunsa, babu wani abin yabo a duniyae nan sai Allah (S.W.T), dukkan yabo da kirari nasa ne, tsarki ya tabbata a gare shi. Sha yabo Sha yabo a zatinsa, da sunayensa, da sifofinsa, da ayyukansa, yana da sunaye mafiya kyau, siffofi mafiya cika, ayyuka mafiya kyau da cika, dukkan ayyukansa suna kewayawa tsakanin falala da adalci. Godiya taka ce, kai kaxai. Ka saukar mana da littafinka, ka sanar da mu girmanka da xaukakarka, ka aiko mana manzonka Muhmamad (S.A.W) Lallai Shi ne Allah sha Yabo
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Allah Mai godiya Abin godewa Shi ne Allah mai godiya abin godewa Shi ne Allah mai godiya.. �To haqiqa Allah mai godiya ne masani� (Albaqra : 158) , �Haqiqa Ubangijinmu mai yawan gafara ne mai godiya� (Faxir : 34) Allah shi ne mai godewa aiki kaxan, ya gafarta zunubi mai yawa, ya ninnika ladar masu tsarkake aiki gare shi, ba tare da wani lissafi ba. �Allah Mai yawan godiya� Yana bawa wanda ya gode masa, ya yi falala ga wanda ya roqe shi, ya ambaci wanda ya ambace shi, wanda ya gode yana da qari, wanda ya kafirce kuwa ya yi hasara. Allah ya ce �Idan kuka gode tabbas zan qara muku, idan kuwa ku ka yi butulci to azaba ta mai tsanani ce� (Ibrahim : 7) �Lallai shi Allah mai godiya ne abin godewa�
Islamkingdom_ar01 Dec, 2019Religion
Allah mai ji Yana jin muryoyi dukkansu, masu rauni da masu qarfi, wata muryar ba ta hana shi ya ji wata, wani mai roqo baya ha na shi jin wani mai roqon. �Mai ji mai gani�.. Yana jin maganarka, don haka ka yi wa kanka hisabi, yana jin addu�arka, don haka ka nace masa, yana ganin ayyukanka, kada ka voye masa komai, ka kyautata, Allah yana son masu kyautatawa. Allah mai gani ne Yana ganin komai, duk qanqantarsa ko girmansa, ko voyayye ciki dare ko rana. Mai ji Yana jin magana, duk da savanin yaruka, da buqatu kala-kala �Mai Gani� Yana ganin tafiyar baqar tururuwa a cikin duhun dare, a kan kurman dutse. Yana ganin abin da yake qasan bakwai, kamar yadda yake ganin abin da yake saman bakwai. Mai ji mai gani Babu wani abin da yake voye masa, babu wani abin da yake guje masa. Haqiqa shi mai ji ne mai gani
Da88mobicom
Hitclub
Nhà Cái 7fun7
Book Planets
Level Up Fashions
Zomclub Official
Kèo Nhà Cái
Cv444
Skyline Builder Wa
Mu88 Today